Bankado cin hanci a sashen tsaron Najeriya | BATUTUWA | DW | 04.12.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Bankado cin hanci a sashen tsaron Najeriya

Kungiyar farar hula ta Cislac ta fitar da rahoto a kan gano matsalar rufa-rufa ga yadda ake gudanar da harkar kasasfin kudi na sashin tsaro, musamman bada kwangilolin sayo kayayyaki, matsalar da ke kawo cikas ga tsaro.

Manyan hafsoshin sojin Najeriya

Manyan hafsoshin sojin Najeriya

A Najeriya kungiyar farar hula ta Cislac ta fitar da wani rahoto a kan gano matsalar rufa-rufa ga yadda ake gudanar da harkar kasasfin kudi na sashin tsaro, musamman bada kwangiloli na sayo kayayyaki, matsalar da ta ce na kawo cikas ga kokarin aiwatar da sauye-sauye a wannan sashi na tsaron kasar. 
Wannan rahoto da kungiyar ta Cisilac ta kadammar a Abuja sakamako ne na bincike mai zurfi a kan daukacin batun kasafin kudi na sashin tsaro a Najeriyar, wanda fakewar da ake da cewa ba’a son bayyana yadda aka yi da kudadden da aka ware wa yankin, ya sanya gano yadda wasu jami’ai ke tafka mummunar cin hanci da rashawa.

Manyan hafsoshin sojin ruwan Najeriya

Manyan hafsoshin sojin ruwan Najeriya

Abin tada hankali shi ne yadda lamarin ke shafar kalubale na rashin tsaro da Najeriya ke fuskanta a yanzu, domin rashin sanin abinda ya haifar da matsaloli mabambanta, kama daga rashin isassun kayan aiki ga sojoji, da ya jawo ake  afka wa sojojin, da sauran al'ummar Najeriya. Mr Salaudeen Hashim manaja ne a kungiyar Cislac mai kula da harkar kasafin kudin sassan tsaro na kasar.
Tun daga shekara ta 2015 dai ake ganin kari a fannin kudadden da ake kasafta wa a bangaren tsaro a Najeriya, musamman saboda tarin  kalubalen da kasar ke fuskanta, kama daga na kai hare-haren Boko Haram izuwa ga ‘yan bidiga da masu garkuwa da jama’a da ma karuwar fashi a gabar tekun Guinea. To sai dai binciken ya nuna cewa karin bai nuna an gani a kasa ba.  Domin bincike ya gano cewa za’a samu kari na kudadden da ake kasafta wa a fannin tsaro daga kashi 37.1 zuwa 37.6. Dr Suliaman Shuaibu Shinkafi mai fashin baki ya bayyana hatsarin da ke tattare da hakan.
Batun kebe kudadde a matsayin na sashin tsaro da ba’a bincika su, ya zama salo a Najeriya, daga ofishin shugaban kasa zuwa sashin sojoji da ma gwamnonin jihohi a yanzu, ta kai ga hatta wasu shugabanin kanana hukumomi da manyan daraktoci na kebe irin wadannan kudade. Amma ga Mallam Yusha’u Aliyu, masani a fannin tattalin arziki, ya bayyana illar wannan ga kokarin tabbatar da nagartaccen tsarin kasa.

A yayin da ya kamata a samu ci gaba bisa ga karin yawan kudadden da ake kasafta wa ga Auwal Musa Rafsanjani shugaban kungiyar ta Cislac, ya ce sun gano cewa karin yawan kudadde ga fannin tsaro, na nufin samar da kari ta hanyar cin hanci da sata ga jami’an sojoji da ke cika aljihunsu, domin ba hanyar fayyace gaskiya, don haka cin hanci kawai karuwa yake a fannin tsaro.
Ko da yake daraktan kungiyar yaki da cin hanci na Transparency International ya yaba wa yunkurin shugaban Najeriya na sa ido a kasafin da ake baiwa sashin tsaro, amma fa ya ce rashin yin ta maza wajen hukunta masu laifi, na barin kafa ta ci gaba da sace dalla bilyan 15 da ake ficewa da ita daga kasar.

Sauti da bidiyo akan labarin