1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin Sallah karama cikin yanayi na annoba

May 24, 2020

Miliyoyin al'umar Musulmi a duniya na bikin Sallah Karama a wannan Lahadin, bikin da bisa al'ada ke zuwa bayan kammala Azumin watan Ramadana. Wasu kasashe kuwa Asabar suka yi.

https://p.dw.com/p/3cgdt
Eid Fest in Nigeria
Hoto: DW/A. A. Abdullahi

A bana dai shagulgula za su bambanta a duniyar da yanda aka saba yin su a baya da akalla ake kwashe kwanaki uku, saboda halin da ake ciki na annobar corona.

Kasar Indonesiya, da ta fi kowace kasa yawan al'umar musulmi da yawansu ya zarta mutum miliyan 240, na daga cikin kasashen da ke Sallar a yau Lahadi.

Bayanai daga kasar na cewa akwai kimanin mutum dubu 22 da suka kamu da cutar COVID-19, wasu dubu da 350 kuwa suka mutu.

A yau din dai kusan a dukkanin kasashen na duniya, za a gudanar bukukuwan na Sallah ne tsakanin iyali ba tare da haduwa ta jam'i  ko wasanni na al'ada ba.