1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaki da azabtar da mutane a duniya

Uwais Abubakar Idris LMJ
June 26, 2020

A yayin da ake bikin ranar tunawa da mutanen da ake azabtarwa a duniya, a Najeriya matsalar na kara karuwa, baya ga rashin hukunta masu laifin domin zama darasi.

https://p.dw.com/p/3ePlw
Nigeria Kaduna Jungen und Männer aus Koranschule befreit
Bikin ranar yaki da azabtar da mutane a duniyaHoto: Reuters/Television Continental

Har kawo yanzu dai ana fuskantar matsalar cin zarafi da azabtarwa da ma musgunawa mutanen da ba su ji ba su gani ba a Najeriya. Mafi akasari dai wadanda ke hannun jami'an tsaro sun fi fuskantar wannan matsala, ta yadda ake gana musu azaba a matsayin hanyar tatsar bayanai daga gare su. Nuna karfin daga jami'an tsaron dai ya kai mataki na kololuwar tabarbarewa a shekarun baya-bayan nan.

Fitowar kafofin sada zumunta na zamani, ya taimaka wajen sanin wadanda ke dandana azaba a hanun irin wadanan jami'ai. A shekarar 2017 Najeriya ta kafa doka da ta haramta ganawa duk wani dan kasar azaba, dokar da kungiyoyin kare hakin dan Adam ke korafin cewa har zuwa yanzu babu koda jami'in tsaro daya da aka hukunta. 

A Najeriya dai hukumomi da aikinsu ne batu na kare hakkin dan Adam sun kasance masu nazari a kan abubuwan da ke faruwa. A kokari na kawo gyara, hukumar kare hakin dan Adam ta Najeriyar na kan gaba a wannan aiki. Ana cike da fata cewa  samun karin matsin lamba ga gwamnati a batun ganawa mutane azabar, zai iya yin tasiri na aikin da dokar da aka kafa a kasar don hukunta masu laifi,abin da zai zama babban darasi ga na baya.