1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Labarin Wasanni 22.08.2022: Bayern ta kidima Bochum a gida

Lateefa Mustapha Ja'afar AMA(AS)
August 22, 2022

Borussia Dortmunt ta yi kwance da kaya a mako na uku na kakar Bundesliga, a yayin da Bayern ta yi wa Bochum cin wulakanci a gida, Manchester United da Liverpool za su kece raini a wannan Litinin.

https://p.dw.com/p/4FrV8
Kakar Bundesliga | VfL Bochum da FC Bayern München
Kakar Bundesliga | VfL Bochum da FC Bayern München Hoto: Thilo Schmuelgen/REUTERS

A karshen mako an fafata a mako na uku na gasar Premier League ta kasar Ingila, kuma Asernal na ci gaba da zama daram a saman tebur bayan da ta ci wasanninta duka ukun. A fafatawarsu ta karshen mako, Arsenal din ta bi Bornemouth har gida ta kuma caskara ta da ci uku da nema. Ita kuwa Manchester City da ke biye mata a matsayi na biyu, ta tashi wasa canjaras uku da uku da kungiyar kwallon kafa ta Newcastel United. Crystal Palace ta samu nasara a kan Aston Villa da ci uku da daya, yayin da Chelsea ta sha kashi da ci uku da nema a gidan Leeds.

Wasan da zai fi daukar hankali dai shi ne na Manchester United dwannan Litinin ne United din za ta fafata da takwararta ta Liverpool da ita ma ta yi kunnen doki a wasanninta biyu da ta buga. Halin tsaka mai wuyar da United din ke ciki ne ma, ya sanya dan wasan gabanta Marcus Rashford yin kira ga takwarorinsa kan su hada kan su domin ganin sun cire wa kansu kitse a wuta.

An yi ruwan kwallaye a kakar Bundesliga

A gasar Bundesliga ta Jamus kuwa wasan da aka fi ruwan kwallaye a karshen mako na ukun shi ne, wasa tsakanin Bayern Munich da Bochum, inda Bayern din ta yi tattaki zuwa Bochum tare da caskara ta da ci bakwai da nema. Sabon dan wasan Bayern din kana tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Sadio Mane na daga cikin wadanda suk zura kwallaye a ragar Bochum, inda dan kasar Snegal din ya zurawa masu masaukinsu kwalaye biyu cikin bakwai din da suka zura a raga.

Kakar Bundesliga | Bayer Leverkusen da Hoffenheim | Georginio Rutter
Kakar Bundesliga | Bayer Leverkusen da Hoffenheim | Georginio RutterHoto: Vitalii Kliuiev/IMAGO

Tun da fari dai awasan da aka fafata a ranar Jumm'ar da ta gabata, Borusssia Mönchengladbach ta samu nasara a kan Herthe Berlin da ci daya mai ban haushi kana Mainz ma ta bi Augsburg har gida a ranar Asabar tare da lallasa ta da ci biyu da daya. Freiburg ma har gida ta bi Stuttgart ta kuma ba ta kashi da ci daya mai ban haushi haka abin ya ke a wasa tsakanin Hoffenheim da ta bi Levekusen har gida ta kuma lallasa ta da ci uku da nema.

An tashi wasa canjaras tsakanin Wolfsburg da Shalke, yayin da aka tashi kunne doki daya da daya tsakanin Eintracht Frankfurt da Cologne. Union Berlin uku ta lallasa RB Leipzig ne da ci biyu da daya. Sai wasan da aka yi baya ba zani wanda kuma shi ne tashar DW ta kawo muku a ranar Asabar din karshen mako, tsakanin Borussia Dortmund da Werder Bremen, inda Bremen din ta bi Dortmund har filin Signal Iduna Park ta kuma lallasa ta da ci uku da biyu. Tun da fari dai Dortmund din ce ta fara zira kwallaye biyu a ragar Bremen, kafin ana daf da tashi wato mintoci 89 da fara taka leda, Bremen din ta yi wa Dortmund baya ba zani inda ta zira kwallaye uku cikin mintuna biyar kacal.

Garcia ta daga kambun Cincinnati Open

Shararriyar 'yar wasan kwallon tennis din nan ta kasar Faransa Caroline Garcia ta samu nasarar lashe kambunta na uku a kakar wasanni ta bana a gagarumar gasar Cincinnati Open da ake yi kafin gasar US Open a Lahadin karshen mako, abin da ya ba ta damar sake komawa cikin shararrun 'yan wasan tennis mata 20 na duniya.

French Tennis Open 2018 | Angelique Kerber, Deutschland
Hoto: Reuters/P. Rossigniol

Mai shekaru 28 a duniya Garcia ta kasance ta hudu cikin shararrun mata ma su buga kwallon na tennis a shekara ta 2018, sai dai ta samu koma baya sakamon wasu matsaloli da kuma ciwon da ta ji a kafarta. Cikin watan Mayu ne dai ta dawo wasa bayan ta warke a matsayi na 79, sai dai nasarorin da ta samu sun taimaka mata wajen komawa matsayi na 17.

Shi kuwa shararren dan wasan tennis na Jamus Alexander Zverev ba zai samu damar halartar gasar ta US Open ba, sakamkon rauni da ya ji idon sawunsa. Rahotanni sun nunar da cewa Zverev ya samu raunin ne a gasar French Open da ta gudana, inda kuma ake fatan zai samu damar fafatawa a gassar Davis Cup group phase da za ta gudana a birnin Hamburg na Jamus din da ke zaman mahifarsa.

A farkon watan Yunin ne dai Zverev mai shekaru 25 a duniya da kuma ke zaman na biyu a jadawalin shararrun 'yan wasan tennis din na duniya, ya murgude idon sawunsa yayin da suke fafatawa da Rafael Nadal abin da ya tilasta yi masa aiki a idon sawun.