Batun nukiliya a Iran | Labarai | DW | 16.08.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Batun nukiliya a Iran

A dai-dai lokacin da takunkumin ƙasashen duniya ya fara aiki kan Iran, ƙasar ta sanar da gina wasu sabbin tashoshi.

default

Tashar nukiliyar Iran ta Isfahan.

Ƙasar Iran tace za ta gina sabbin tashoshin nukiliya guda goma a baɗi. Shugaban kula da ayyukan nukilyar ƙasar Ali Akbar Salehi, shine ya bayyana haka a hirar da ya yi da talavijin ɗin gwamnatin ƙasar. Inda yace tashar farko za'a fara gina tane a watan maris na baɗi, to amma bai yi ƙarin haske bisa wuraren da za'a kafa tashoshin ba. Izuwa yanzu ƙasar Iran tana da tashoshin haɗa nukiliya a Ifahan da Natanz a tsakiyar ƙasar, yayinda ake ci gaba da gina tasha ta uku yanzu haka. Sanarwar da ƙasar Iran ta bayar ayau, wata bijirewace ga matsin ƙasashen yamma, waɗanda suke buƙatar Iran ta tsaida shirin ta na nukiliya. MDD ta azawa Iran takunkumi har sau kashi huɗu, inda suke zargin ƙasar dacewa inganta nukiliyar da take yi, yunƙurine na haɗa makamai abinda ita kuwa ta musanta.

Mawallaf: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu