1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar yunwa a kasashen hamsin na duniya

Monir Ghaedi ARH/LMJ
October 15, 2021

Wani sabon rahoto kan matsalar yunwa a duniya, ya ce kasashe 50 na na fuskantar babbar barazanar karancin abinci. Rahoton ya ce sauyin yanayi da tashe-tashen hankula na cikin abubuwan da ke ta'azzara matsalar.

https://p.dw.com/p/41gkN
Hunger im Sahel Bildergalerie Tschad
Sauyin yanayi da rikice-rikice, na daga cikin abubuwan da ke janyo karancin abinciHoto: Andy Hall/Oxfam

Rahoton wanda shi ne karo na 16, ya nuna barazanar rashin zaman lafiya da ta zama karfen kafa ga wasu kasashen duniya, a matsayin wani babban jigo na hana Majalisar Dinkin Duniya cimma muradinta na yaki ko kawar da yunwa a duniya nan da shekara ta 2030. Joe Mzinga shi ne shugaban wata kungiyar kananan manoma na gabashi da kudancin Afirka, ya yi wa DW karin bayani kan yadda matsalar ke shafarsu: "Idan akwai rikici wanda girmansa ke kai wa ga daukar makamai tsakanin bangarori biyu, wato [A lokacin yaƙi,] ba za mu iya ci gaba da samar da abinci kamar yadda aka saba ba kuma ba za mu iya shiga kasuwanni kamar yadda muka saba ba."

Karin Bayani: Yajin aikin masu kai abinci kudancin Najeriya 

Binciken wanda aka fitar a Allhamis din wannan mako, na zuwa ne makwanni kalilan bayan Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da bayanan da ke nuna cewa adadin mutanen da ba sa samun abinci mai gina jiki a bara ya haura miliyan 320 zuwa biliyan biyu da miliyan 400, wanda ya kai kusan kashi daya bisa uku na mutanen duniya. Miriam Wiemers na cikin mawallafa sabon rahoton na mastalar yunwa a duniya a 2021: "Wannan sabon rahoton, yana sake nuna alamun cewa, yunkurin yaki da yunwa nan da shekara ta 2030 ya samu komabaya. Komawar hannun agogo baya kan kawar da yunwa, yana kara haifar da rikice-rikice masu yawan gaske da kuma karin matsalar sauyin yanayi ko cututtuka."

Somalia Hungersnot Schlange von Menschen vor Ausgabe von Lebensmitteln in Mogadishu
Tashe-tashen hankula a Somaliya, na daga cikin dalilan da suke janyo yunwa a kasarHoto: dapd

Tasirin sauyin yanayi yana kara fitowa fili, amma duniya ba ta samar da wata ingantacciyar hanyar da za ta iya rage ko magance matsalar ba. Annobar COVID-19 wacce ta zama karfen kafa ga duniya baki daya, na nuna yadda ake cikin mawuyacin hali a duniya da sakamakon alakar kiwon lafiya da tattalin arziki a cewar Miriam Wiemers: "Yaki da yunwa ba shi ne kawai burin da kasashen duniya suka sa a gaba ba, yana shafar hatta hakkin mutane na samun isasshen abinci mai gina jiki. Samun abinci shi ne hakkin dan Adam na asali, don haka a yanzu muna da miliyoyin mutane a duniya wadanda ake take hakkinsu kullum."

Karin Bayani: Najeriya na fuskantar barazanar yunwa

Kasar Somaliya mai fama da hare-haren mayakan al-Shabaab da rikicin yanki da kabilanci na mataki na 116, wannan ya sa ta zama kasar da ta fi fuskantar bala'in yunwa a rahoton na bana, sai kuma Yemen da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Chadi da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Madagaska da Laberiya da Haiti da saliyo da Mozambik da Congo Brazabil da Najeriya da Afghanistan a mataki na 103.