1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Masu safarar abinci zuwa Kudu na yajin aiki

Muhammad Bello MAB
February 25, 2021

Hadaddiyar kungiyar masu safarar abinci da dabbobi daga Arewa zuwa Kudancin Najeriya ta dakatar da harkokinta bayan karewar wani wa'adi da ta bai wa hukumomin Kasar kan wasu kokensu da suke son a magance.

https://p.dw.com/p/3pvdw
DW eco@africa solarbetriebene Kühlschränke
Hoto: DW

Yajin aikin na nufin dakatar da safarar dukkanin kayayyakin abinci da dabbobi zuwa kudu har tsawon kwanaki bakwai. Tuni Jama'a suka fara hangen illolin da ka iya biyo bayan wannan mataki da suka hada da na tsaro da 'yunwa da na zamantakewa a Najeriya. Ba tun yanzu ba ne masu safarar kayayyakin abincin ke kokawa kan cin zarafi da suke fuskanta musamman ma a jihohin Kudu da suke ketarawa don kaiwa zangon da suka nufa, tare da kuma takurawar Jami'an tsaro da kan sa shingaye kan hanyoyi ba bisa umarnin hukumomi ba.

Masu safarar sun ta kokawa kan yadda suke rasa rayukansu ta hanyar farmakin wasu kabilu, tare tashin hankali a wani bangare na kasa, inda ake afka musu tare da motocinsu ,da ma kayayyakin da motocin ke dauke da su. Tuni ma Shugaban gamayyar Kungiyoyi Alhaji Abdullahi Awwal ya ce sun kasa sun tsare a daukacin hanyoyin da ke zuwa kudancin Najeriya.

Nigreria Fulani-Nomaden
Da alama za a samu karancin shanu a kasuwanni dabbobi na kudancin NajeriyaHoto: AFP/Luis Tato

 Munin wannan mataki na dakatar da kai kayayyakin abinci ga Jama'ar kudu ya fara bayyana, inda wasu mazauna birnin Fatakwal da ke kudancin kasar suka fara korafi kan yiwuwar karancin abinci.

An fara fargabar tsadar abinci a kudancin Najeriya

Nkiruka Nnadi na cewa: "Bala'in da hakan zai haifar ba karami ba ne, domin ko ba wannan yajin aiki, wahala wajen ciyar da kai ba karama ba ce, musamman ma a birnin Fatakwal da ke zaman birnin mafi tsadar rayuwa: Sau tari iyalai kan ci sau daya a rana da kyar, na tuna lokacin zanga zangar ENDSARS ,wahalar da aka sha ba karama ba ce, wasu ma ba sa samun abinci. Yanayin ya tsananta matsalar tsaro sosai, domin duk mai rai dole ya san yadda zai sa wani abu a ciki.

Ita ma Madame Precious Ahiako ta ce: " Yawa-yawan abinci da muke ci na zuwa ne daga Arewa, kuma mun san wahalar da muka sha a wani lokaci, inda tumatir da albasa da sauran su suka yi wani tashin farashi, lamarin fa ba zai kyau ba, ya kamata gwamnati ta sa baki."

DW eco@africa solarbetriebene Kühlschränke
Mazauna Fatakwal na fargabar haihawar farashin abinci a kasuwanniHoto: DW

 A kasuwanni dai, farashin kayayyakin abinci bai fara tashi ba, musamman ma ganin cewar wannan mataki na dakatar da kai kayayyakin ya fara aiki ne a wannan Litinin (25.02.2021). Barister Jalo, dan siyasa kuma mai sharhi kan al'amura a Najeriya ya ce tattaunawa da kungiyar ta ma su safarar abinci ta fi tattaunawa da 'yan ta'adda da gwamnatocin jihohi ke kokarin yi.