Barazanar ISIS wajen wargaza Iraki | Zamantakewa | DW | 26.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Barazanar ISIS wajen wargaza Iraki

Rikicin fafutukar kwace madafan iko da kafa kasar Islama da ISIS ke yi na ci gaba da bude wata kafa na wargajewar kasar Iraki, wanda aka kasa samun hanyar warwareshi.

Kungiyar Tarayyar Turai da kasashen yammacin duniya dai na ganin muddin ba a gaggauta magance wannan matsala ba to kuwa za ta bazu zuwa sauran sassan kasar da ma kasashen da ke makobtaka ta da ita. Wannan ne ma ya sanya sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya shirya wata ziyara ta ba zata zuwa Irakin don tataunawa da Firaminista Nuri al-Maliki da nufin shata hanyoyin warware rikici.

DW.COM