Iran ta soki lamirin shigar Amirka Iraki | Labarai | DW | 22.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran ta soki lamirin shigar Amirka Iraki

Shugaban addinin Musulunci na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ayatollah Ali Khamenei ya nuna kin amincewarsa da shigar dakarun Amirka makwabciyarsu Iraki

Dakarun na Amirka dai na kokarin shiga Irakin ne domin shawo kan matsalar 'yan ta'addan ISIS da suka addabi kasashen Iraki da Siriya. 'Yan tawayen na ISIS da kuma Musulmi mabiya Sunna da ke adawa da mahukuntan Tehran dai sun kwace garuruwa masu muhimmanci da dama a Iraki a 'yan kwanakin nan. Sai dai duk da wannan adawa da mayakan ke yi da Tehran Kamfanin Dillancin Labarai na

Jamhuriyar Musulunci ta Iran din IRNA ya ruwaito Sayyid Khamenei na cewa ya na matukar adawa da shigar Amirka da dangoginta cikin shirgin kasar Iraki ya na mai cewa babban rikicin da ke faruwa a Iraki ana yinsa ne tsakanin 'yan kasar da ke son zama a karkashin ikon Amirka da kuma wadanda ke son Iraki mai cikakken iko.

Ayatollah Ali Khamenei ya yi zargin cewa Amirka ce kawai ke son ta dora wanda take so akan mulki a kasar ta Iraki. Iran dai ta ce a shirye take ta ba da agajin sojoji domin su taimaka wajen fatattakar 'yan tawayen ISIS daga Irakin in har an bukaci hakan daga gareta.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Pinado Abdu Waba