Fafutukar ISIS ta hanyoyin sada zumunta | Siyasa | DW | 23.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Fafutukar ISIS ta hanyoyin sada zumunta

Ƙungiyar masu kishin addini ta Iraƙi ISIS na yin amfani da hanyoyin sada zumunta domin bayyana manufofinsu.

A fafutukar da ta ke yi na ƙwace mulki da yankunan ƙasar Iraƙi domin kafa wata ƙasa ta Islama. Ƙungiyar 'yan gwagwarmayya 'yan Sunni masu kishin addini wato ISIS, ta ƙaddamar da wani shiri na farfaganda ta hanyoyin sada zumunta irinsu Twitter da Facebook domin bayyana wa duniya matsayin ƙungiyar.

Abin da za a iya lura da shi a shafunka shi ne da farko an nuno wasu hotunan na mayaƙan ƙungiyar ta ISIS su tara fuskokinsu a rufe da rawani, ɗauke da manyan bindigogi. A gaba wani shafin ya nuna wasu 'yan gwagwarmayyar su kusan 20 ɗauke da makamai suna shirin bindige wasu matasan.

Hotunan da ƙungiyar ta watsa sun ɗauki hankali jama'a

Waɗannan hotunan kuma waɗanda aka watsa ta hanyar shafin Yotube da Twitter sun yi yawo a cikin ƙasashen duniya da dama tare da katse hanzarin jama'ar dangane da yadda masu kishin addini ke aikata mumunar ta'addi a kan farar hula.Yassin Musharbash wani ƙwarare a kan harkokin ta'addanci da ke aiki da jaridar Die Zeit ta Jamus ya ce da walaki a cikin lamarin na ISIS.

''Wa ya buɗe musu kuma ya tsara musu aikin a kan Twitter, farfagandi ce mai ƙarfin gaske suke yi.''

To sai dai a yanzu gwamatin Iraƙin a yankunan da ƙungiyar ta ISIS ta ƙwaci iko da su,ta tsinke hanyoyin sadarwa na intanet amma duk da haka a wasu yankunan ana iya samu ta hanyar tarmamun ɗan adam.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe

Sauti da bidiyo akan labarin