Barazanar ficewar Girka daga kasashen Eurozone | Labarai | DW | 26.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Barazanar ficewar Girka daga kasashen Eurozone

Jam'iyyar adawa ta Syriza a Girka da ke da tsattsauran ra'ayin sauyi ta samu nasarar lashe zabukan kasar da aka gudanar.

Jam'iyyar dai na tsananin adawa da tsauraran matakan tsuke bakin aljihu da kasashen da ke ba da bashi suka dora kasar a kai. Sai dai rahotanni sun nunar da cewa ta dan samu nakasu a kujerun majalisar dokoki wanda ya sanya ba za ta iya gudanar da mulki ita kadai ba tilas ne sai ta kafa gwamnatin hadin gwiwa da wata jam'iyyar. A jawabin da ya yi shugaban jam'iyyar ta Syriza Alexis Tsipras ya sha alwashin sake tattauna batun bashin da aka bai wa kasar domin ceto ta daga durkushewa, bashin da ya ce ya matukar takura mata na tsahon shekaru. A nasa bangaren Firaministan kasar ta Girka mai barin gado Antonis Samaras ya nuna fargabarsa kan ci gaba da kasancewar Girkan cikin kasashen da ke amfani da kudin Euro wato Eurozone da ma kungiyar Tarayyar Turai EU, yana mai cewa batun dorewarta cikin wadannan kasashe da kungiyar na cikin garari. A wannan Litinin din ne dai ministocin kudi na kungiyar Tarayyar Turan za su tattauna batun zaben na Girka da abunda ka iya biyo baya a birnin Brussels na kasar Belgium.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal