Barack Obama ya yi kiran tattaunawa da Iran | Labarai | DW | 20.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Barack Obama ya yi kiran tattaunawa da Iran

Shugaban na Amirka ya yi kira ga hukumomin na Iran da su ba da haɗin kai ga ci gaban tattauna shirin nukiliya na ƙasar.

Shugaba Barack Obama ya gargaɗi shugabannin ƙasar ta Iran da su yi amfani da damar da ake da ita mai cikke da tarihi domin ganin an cimma matsaya ɗaya a kan shirin nukiliya na ƙasar

Obaman dai ya ce kwanaki na gaba masu zuwa za su kasance masu mahimmanci, kana kuma ya ce an samu ci gaba wajen tattaunawa sai dai har yanzu ya ce akwai saɓanni da ke tsakaninsu da ƙasar ta Iran a kan batun.