Bankuna sun fara aiki a Girka | Labarai | DW | 20.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bankuna sun fara aiki a Girka

Duk da cewa bankunan na bude, mahukunta sun kayyada yawan kudin da za su iya cirewa bisa tanadin sharuddan da Turai ta gindaya.

Da safiyar Litinin ne aka bude bankunan Girka bayan da aka rufe su na wani tsawon lokaci, sai dai har yanzu ba komai bane masu ajiya a bankin zasu iya yi, kuma an kayyade yawan kudin da zasu iya cira daga ajiyar tasu. Bacin haka kuma, kayayyakin masarufi za su cigaba da tsada sakamakon karin harajin da majalisar dokokin kasar ta amince da shi ranar alhamis din da ta gabata, wanda ya kasance daya daga cikin sharuddan da masu bayar da rancen suka gindayawa Girkar.

Majalisar dai ta amince da aiwatar da wasu sauye-sauye a tsarin kudin fenshow da ma daina bayar da damar zuwa fenshown da wuri.

Duk wannan na zuwa ne bayan da aka rantsar da sabbin jami'an gwamnati biyar a gwanatin hadin gwiwar kasar, wadanda suka maye gurbin 'yan jam'iyyan Siryza domin hudu daga cikinsu sun yi watsi da tayin Turai na kubutar da Girkar daga bashi, a yayin da daya ta yi murabus tun kafin a kai ga zaben