Bankin Duniya ya ware kudi don yakar Ebola | Siyasa | DW | 05.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bankin Duniya ya ware kudi don yakar Ebola

Barazanar yaduwar cutar Ebola na firgita jama'a musamman a yankin yammacin Afirka. Sai dai yanzu da aka sami wannan kudi babbar tambayar ita ce ko tallafin zai yi nasarar yakar cutar yadda ya kamata.

Kimaninn dalar Amirka miliyan 200 ne Jim Yong Kim wanda ke jagorantar Bankin Duniya ya ayyana warewa a matsayin wani tallafi na gaggawa ga kasashen Laberiya da Saliyo da Guinea a kokarin da ake yi na shawo kan kwayoyin cutar ta Ebola, ga kuma karin wasu dala miliyan 60 daga Bankin raya kasashen Afrika.

A baya ma a shekarar 1987 Dakta Kim ya bada gudunmawa sosai wajen yaki da cutar tarin TB mai saurin bazuwa a kasar Haiti ga mutane kusan 100.000. Abin tambaya shine ko ta wace fiska ake son amfani da wadannan kudade a wannan lokaci? Kim ya yi karin haske.

"Wadannan kudade za a yi amfani da su kan ababan da akafi bukata yanzu, misali samar da magunguna da ma'aikatan jiyya da kuma tallafawa mutanen da suke fiskantar barazana ta koma bayan tattalin arziki sakamakon wannan annoba."

Ebola Ausbruch in Uganda

Kwayar cutar Ebola

Tun dai daga ranar 1 ga watannan na Agusta ne Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta kaddamar da wani shiri na kar ta kwana inda aka ware dala miliyan 100 dan tallafawa kasashen Guinea da Laberiya da Saliyo kasashen da wannan annoba ta fi addaba.

"Hakki ne da ya rataya a wuyanmu mu kula da wannan yanki, za mu yi duk abin da za mu iya ,ba wai kawai mu bada tallafi ba har ma da samar da wani tsari na kula da lafiya da mutanan wadannan kasashe uku suka cancanci samu."

Ma'aikatan jiyya da dama ciki kuwa ha rda manyan likitoci da suke kula da irin wadannan marasa lafiya ta Ebola sun riga mu gidan gaskiya ,amma a cewar wasu ma'aikatan jiyyar irinsu Richard Amos da ke aiki a birnin Monroviya ba su da isassun kayan aiki ne shi ne dalili.

"Ma'aikatan lafiya suna tunanin ba sa samun kariyar da ta dace, saboda haka ma'aikatan jiya har ma da wasu likitocin sun gwammace su zauna a gida."

Da alama dai yadda kasashen duniya suka tashi yaki da wannan annoba ta Ebola da wuya a cimma nasarar da ta dace kamar lokacin yaki da cutar tarin TB, kasancewar hukumar ta WHO ya zuwa yanzu cikin wannan tallafi data bayyana dala miliyan 30 ne kawai ta shiga hannunta.

Mawallafa: Peter Hille/Yusuf Bala
Edita: Pinado Abdu Waba

Sauti da bidiyo akan labarin