Bankin ADB ya bawa Burundi rancen makuden kudade
January 16, 2006Talla
Bankin raya kasashen Africa, wato ADB a turance ya bawa kasar Burundi rancen kudi har dalar Amurka miliyan 17 da digo biyar.
A cewar bankin na ADB, kasar ta Burundi zata yi amfani da wadannan kudaden ne don samar da kyakkawan ruwan sha da kuma hanyoyi ne a karkara.
Hakan dai ya biyo bayan lalacewar da yawa daga cikin hanyoyin ne da kuma bututun ruwan shan, a sakamakon yakin basasa na tsawon shekaru 12 da kasar ta fuskanta.
Bankin dai na ADB, dake da babban ofishin sa a kasar Tunisia, an kafa shine a shekara ta 1964 don bawa gwamnatoci da kamfanunnuka masu zaman kansu a nahiyar rance, don bukasa aiyukan raya kasa.