Ban kwana ga jagoran yaki da wariyar launin fata
December 12, 2013Talla
Shugabannin kasashe da na gwamnatoci daga sassa daban daban na duniya ne suka halarci addu'oin ban kwana ga jagoran fafutukar yaki da wariyar launin fata a Afirka Ta Kudu, inda daga baya kuma sauran jama'a da kuma baki daga ketare suka bi sahu wajen nuna alhininsu ga marigayi Nelson Mandela.