Al′umma na bankwana ga Nelson Mandela | Siyasa | DW | 11.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Al'umma na bankwana ga Nelson Mandela

Dubban al'ummar Afirka ta Kudu sun hallara a ginin Union Building inda aka ajiye gawar Nelson Mendela domin bankwana na ƙarshe.

Tun da misalin ƙarfe bakwai na safiyar Larabar nan ce dubun-dubatar al'ummar Afirka ta Kudu suka hallara kan tituna da ma ginin nan na Union Buldings da ke wajen Pretoria, babban birnin ƙasar don yin bankwana da madugun yaƙi da wariyar launin fata na ƙasar Nelson Mandela wanda Allah ya yi wa cikawa a ranar Alhamis ɗin makon jiya.

Juyayi na ƙasa baki ɗaya ga gawar Nelson Mandela

Duk da cewar an yi rana sosai yau a birnin na Pretoria, hakan bai sa jama'a ba sun gajiya ba inda suka ɗau tsawon lokaci kan layuka don shiga ginin na Union Buldings inda nan ne aka ajiye gawar ta Mandela bayan da aka ɗauko ta daga wani asibitin soji don bai wa jama'a sukunin yin bankwana da shi. Shugaba Jacob Zuma ne ya shige gaba wajen ganin gawar wadda ke cikin akwati sanye da irin rigar nan samfurin ƙasar Indunisiya wadda aka san Mandela da ita, inda daga bisani mai daƙinsa ta yanzu Graca Machel ta biye masa baya sai kuma sauran 'ya'yansa gami da shugabannin ƙasashen Afirka da sauran baƙi da aka gayyata. Daga bisani kuma al'ummar ƙasar suka bi sahu wajen shiga ginin don ganin gawar. Jen Hewitt na daga cikin wanɗanda suka bi layi don shiga ginin inda ta yi bankwana da Mandela. ga kuma abin da ta ke cewa.Ta ce ''Jimawa kan dogon layi da bukukuwan da ake yi duk sun dace. Dole ne mu karrama wannan mutumin domin kuwa muna ganinsa da ƙima sosai. A ce mutum ya rayu a lokacin da Mandela ke da rai shi kansa wani babban abu ne. Zuwa wajen nan don yin bankwana da shi wani abu ne mai kyau.''

Dongon layi na jama'a a gaban ginin domin ziyartar gawar

Baya ga Jen, dubban 'yan ƙasar sun samu sukunin ko dai na shaida sanda aka wuce da gawar ta Madiba ta kan titunan Pretoria ko ma isa ginin Union Buildings don yin tozali da ita da ma bankwana da shi inda da damarsu ke sanye da riguna da ke ɗauke da hotonsa.Tuni dai al'ummar ƙasar suka fara cewar lokaci ya yi da za su danne zuciyarsu dangane da wannan rashi da suka yi su kuma ci gaba da dafa wa juna daga inda Mandela ya tsaya don tabbatar da ƙasar kan turbar da Mandela ya ɗorata tun bayan da aka sallame shi daga kaso. Wata dattijuwa 'yar Afirka ta Kudun mai suna Sharley Harrison ta ce ''dole ne su ɗora daga inda ya tsaya. A nata ɓangaren ta ce ta na ƙoƙarin taimaka wa 'yarta mai yi mata hidima don ganin ta samu sana'ar yi, inda ta ƙara da cewar daga irin haka ake fara wajen tallafa wa juna.''A gobe Alhamis da jibi Jumma'a ma dai za a kewaya da gawar ta Mandela kan titunan na Pretoria sannan a kai ta ginin na Union Buildings domin jama'a su ci gaba da yin bankwana da ita sannan a ranar Asabar ce ake sa ran kai gawar Mandela zuwa ƙauyensu na Qunu domin yi mata sutura ranar Lahadi kusa da kusheyun 'ya'yansa guda uku da suka riga suka rasu.

Daga kasa za a iya sauraron wannan rahoto

Mawallafi : Ahme Salisu
Edita : Abdourahamane Hasssane

Sauti da bidiyo akan labarin