Ban Ki-moon zai halarci taron koli na AU | Labarai | DW | 29.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ban Ki-moon zai halarci taron koli na AU

Babban magatakaradan Majalisar Dinkin Duniya zai yi tattaki zuwa cibiyar AU a Addis Ababa, inda zai tattauna da shugabannin Afirka kan matsalar Boko Haram

Sakatare janar na MDD Ban Ki-moon zai halarci taron shugabannin kasashen kungiyar Gamayyar Afirka ta AU da za a gudanar a birnin Addis Ababa na kasar Ethiopiya. Kakakinsa Stephane Dujarric ne ya shaida wa manema labarai haka a birnin New York na kasar Amirka.

Taron zai mayar da hankali ne kan kungiyar Boko Haram da a yanzu ta addabi tarayyar Najeriya. Ban Ki Moon, ya ce zai yi kokarin karfafa wa shugabannin Afirkan gwiwa wajen nemo mafita kan barazanar da Boko Haram ke haddasawa a kasashen nahiyar a yanzu.