Ban Ki-Moon ya kai ziyara a kasar Libiya | Labarai | DW | 11.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ban Ki-Moon ya kai ziyara a kasar Libiya

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya isa a birnin Tripoli na kasar Libiya a wannan Asabar din, a wani mataki na karfafa tattaunawa tsakanin bengarorin kasar.

Cikin wannan ziyara da ta kasance tamkar ta bazata, Ban Ki-Moon ya isa kai tsaye ne ga wani babban Otel da ke birnin na Tripoli domin tattaunawa da hukumomin wannan kasa a cewar wata majiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta UNSMIL dake kasar ta Libiya.

A karshen watan Satumba ne dai da ya gabata, wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a wannan kasa Bernardino Leon, ya samu nassarar hada 'yan majalisu na bangarori daban-daban na wannan kasa a karo na farko, wanda ake ganin wani babbar ci gaba ne. A wannan ziyarar, Ban Ki-Moon yayi kira ga bengarorin kasar da su koma ga tattaunawa.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Pinado Abdu Waba