Ban Ki-Moo zai kai ziyara a kasar Burundi | Labarai | DW | 22.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ban Ki-Moo zai kai ziyara a kasar Burundi

Wasu mutane dauke da makammai sun hallaka mutun biyu da a wani gari da ke kauyan Bujumbura yayin da ake shirin isowar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya.

UN Generalversammlung - Ban Ki-moon

Ban Ki-moon

A cewar Célestin Singirankabo da ke a matsayin shugaban gundumar Gisozi da ke cikin jihar Mwaro, mutanen an kashe su ne da yannnacin ranar Lahadi a yankin Kiyange da ke a nisam km a kalla 50 da Bujumbura babban birnin kasar ta Burundi.

Kawo yanzu dai fiye da mutane 400 ne suka rasu sakamakon rikici a kasar tun da daga watan Afrilu bayan da Shugaban kasar Pierre Nkurunziza ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takara a wani sabon wa'adin da ake wa kallon haramtacce. A ranar Talata ne dai aka tsara Ban Ki-Moon zai gana da shugaban kasar ta Burundi a ziyarar da zai kai a wannan kasar.