1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bambancin ra'ayi kan rashin bude wasu iyakokin Nijar

Gazali Abdou Tasawa MAB
March 21, 2024

Hukumomin mulkin sojan Nijar na ci gaba da rufe iyakokinsu da Najeriya da Benin, duk da dage takunkumi da ECOWAS ta yi. Wasu na ganin cewar matakin ya jefa talakawa cikin kuncin rayuwa yayin da wasu ke ganin dacewar sa.

https://p.dw.com/p/4dyQ0
Har yanzu zirga-zirga ba ta kankanma a kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar
Har yanzu zirga-zirga ba ta kankanma a kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar NijarHoto: DW/Y. Ibrahim

Kusan wata daya kenan da kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ta dage wa Nijar takunkumin karya tattalin arzikin da ta garkama mata bayan juyin mulki, lamarin da ya bayar da damar bude iyakokin kasar da suka kasance a rufe na tsawon watanni . Hasali ma dai, a hukumance ne gwamnatin Najeriya ta sanar da bude iyakar kasarta da Nijar mai tsawon kilomita 1,500 inda jihohin kasar bakwai ke iyaka da Nijar. Kazalika ta mayar wa Nijar da lantarkin da ta katse tun watanni da dama.

Karin bayani: Nijar: Ba ta sauya ba a kan iyakokin kasar

Danganta ta yi tsami tsakanin Patrice Talon na da Janar Abdourahamane Tiani
Danganta ta yi tsami tsakanin Patrice Talon na da Janar Abdourahamane TianiHoto: Yanick Folly/AFP/Getty Images, ORTN/TÈlÈ Sahel/AFP

Ita ma a bangarenta, Jamhuriyar Benin wacce ke zama hanya mafi kusa wajen shigo da hajojin Nijar daga ketare ta hanyar tashar ruwan Cotonou da ke a nisan kilomita 1000 da Yamai ta bude iyakarta. Sai dai hukumomin mulkin sojan Nijar sun ci gaba da rufe iyakokin kasar da wadannan kasashe biyu.  Bana Ibahim da ke zama dan fafutika mai kusanci da gwamnatin mulkin sojan Nijar ya ce barazanar tsaro ne ke hana hukumomi bude iyakoki da wadannan kasashe.

Rashin bude iyakoki na ci wa wasu 'yan Nijar tuwo a kwarya

'yan Nijar da dama musamman ma mazauna Najeriya da Benin ko kuma na garuruwan kan iyakokin kasashen biyu ne kiraye-kirayen ganin Nijar tza bude iyakoki da wadannan kasashen biyu domin rage wa talakawan kasar radadin rayuwar da suke fama da shi. Malam Alassane Intinikar, wani matashin dan siyasa a Nijar na daga cikin masu wannan damuwa.

Karin bayani: Sojojin sun sanar da bude iyakokin Nijar

Jibia na daga cikin garuruwan da rashin bide iyakar Nijar ya shafa
Jibia na daga cikin garuruwan da rashin bide iyakar Nijar ya shafaHoto: Mohammed Babangida/AP/dpa/picture alliance

Sai dai Moustapha Abdoulaye, wani mai sharhi kan harkokin diflomasiyya na ganin cewar duk da yake Nijar na da shakku kan kasashen biyu, akwai bukatar duba tattaunawa ta ruwan sanyi da kasashen biyu domin warware matsalar. Jama'a sun zura ido su ga yadda gwamnatocin wadannan kasashe uku makwabta kuma 'yan uwan juna na Nijar da Najeriya da Benin za iya warware wannan sabani, wanda ya jefa talakawan kasashensu cikin wani yanayi irin na biri ya gaji mai gona ya gaji.