1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makiyaya 27 sun mutu a harin bam

Abdul-raheem Hassan
January 26, 2023

Rahotanni daga arewacin Najeriya, na cewa wani jirgin sama na sojoji ya sake ababen fashewa kan makiyaya da ke kora shanu a kauyen Rukubi kan iyakar Nasarawa da Benue.

https://p.dw.com/p/4MhuA
Nigeria Kriminalität Gangs Kaduna
Hoto: Stefan Heunis/Getty Images/AFP

Kakakin kungiyar fulani a Najeriya wato Miyetti Allah Cattle Breeders Tasi'u Suleman, ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da makiyaya ke tafiya da shanunsu zuwa Nasarawa daga Benue, inda hukumomi suka kwace dabbobinsu saboda karya dokokin hana kiwo. “Akalla mutane 54 ne suka mutu nan take, wadanda suka jikkata ba su da yawa,” in ji Suleman.

Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule, bai bayyana adadin mutanen da suka mutu ba a hukumance. Amma sun shaida wa manema labarai cewa fashewar bam ne sanadiyyar mutuwar mutanen. Ya zuwa yanzu gwamnati ba ta bayyana wanda ake zargi da hannu wajen fashewar ba, amma ta ce gwamnan ya ce yana ganawa da hukumomin tsaro don tabbatar da zahirin lamarin.

Mai magana da yawun gwamnan Abubakar Ladan, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa
An gudanar da jana'izar jama'a ga wadanda aka kashe a ranar Laraba.

Arewacin Najeriya wanda aka fi sani da Middle Belt, na cikin yankin da ke fama da tashin hankali sakamakon rikicin fulani makiyaya da manoma, wadan da mafi akasi kiristoci ne.

Masana sun ce karuwar jama'a da sauyin yanayi ne suka haddasa mamaye filayen noma wanda ya takaita filayen kiwon shanu.