Bam ya hallaka mutane da dama a Adamawa | Labarai | DW | 02.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bam ya hallaka mutane da dama a Adamawa

Fashewar wani abin da ake zaton Bam ne a wata unguwa a Mubi da ke arewacin jihar Adamawa a Najeriya ya halaka mutane da dama a jiya Lahadi.

Lamarin dai ya faru ne a wani filin kwallo da ke unguwar Kabang kamar yadda wani da ya shaida faruwar lamarin ya bayyanawa wakilinmu na Yola Muntaqa Ahiwa ta wayar tarho, inda ya ke cewa ya ga gawarwaki da dama baya ga wasu da suka jikkata.

Ya zuwa yanzu dai hukumomin jihar ba su yi karin haske ba game da harin na jiya, sai dai mazauna yankin sun bayyana cewa hari ya sake sanya karin fargaba a fadin jihar ta Adamawa.

Babu dai wata kungiya da ta dauki alhakin wannan harin na jiya, sai dai kungiyar nan ta Boko Haram da ke gwagwarmaya da makamai ta sha kai hare-hare na bam a jihar.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe