Bam ya hallaka mai shigar da kara a Masar | Labarai | DW | 29.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bam ya hallaka mai shigar da kara a Masar

Hicham Barakat ya rasu a sakamakon raunukan da ya ji a cikin wani hari da wasu suka kaiwa motarsa a hanyarsa ta zuwa aiki a birnin Alkahira na kasar Masar.

Allah ya yi wa Hicham Barakat Mai shigar da kara na gwamnatin Masar rassuwa a sakamakon raunikan da ya ji a cikin wani harin ta'addanci da bmm da wasu 'yan bindiga suka kai masa a motarsa a birnin Alkahira. Ministan shari'a na kasar ne ya tabbatar da labarin ga manema labarai inda ya ce babban mai shigar da karan ya rasu ne a assibitin da aka kwantar da shi bayan harin da aka kai masa.

Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta fito ta dauki alhakin wannan hari. Sai dai da farko wata kungiya da ba sani ba sosai ta dauki alhakin kai harin a saman face Book kafin ta kuma ta ci tuwon fashi daga baya.

Sai dai a cikin wata sanarwa da ta fitar ran 21 ga watan Mayun da ya gabata reshen kungiyar 'yan jihadi ta IS mai da'awar kafa daular Muslunci na kasar ta Masar ta yi kira ga magoya bayanta da su kaiwa alkalai hari a wani mataki na mayar da martani ga hukuncin rataya da aka zartar akan wasu mutanen kungiyar da aka kama da kaddamar da hare-hare .