Badakalar siyasar Amirka | Labarai | DW | 04.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Badakalar siyasar Amirka

Shugaba Donald Trump na zargin tsohon Shugaba Obama da leken asiri.

USA Präsident Donald Trump Telefonat mit Australiens Premierminister Malcolm Turnbull (picture-alliance/dpa/Pete Marovich/CNP/AdMedia)

Shugaba Donald Trump na Amirka

Shugaba Donald Trump na kasar Amirka, ya zargi tsohon Shugaban kasa Barak Obama da satar bayanan wayarsa a hasumiyar nan ta Trump Tower wanda ke birnin New York, a lokacin da yake dai dai da samun nasarar lashe zaben kasar da aka yi a bara. A wasu sakonni a shafinsa na Tweeter, Shugaba Trump ya bayyana satar bayanan wayar tasa a matsayin mummunan lamari. Amma fa Shugaban na Amirka bai bayar da wata shaida kan zargin ba.

Wasu rahotanni dai na nunin cewa hukumar bincike ta FBI ta nemi takardar izini don sa ido kan mukarraban Trump wadanda ake zargi da yin hulda da kasar Rasha, musamman huldodin da ba a saba irinsu ba. Ya zuwa yanzu dai fadar White House ta Amirkar bata ce komi ba kan wannan batun, haka shi ma bangaren tsohon Shugaba Obama.