Badakalar cin hancin tsakanin alkalan Najeriya | Siyasa | DW | 28.02.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Badakalar cin hancin tsakanin alkalan Najeriya

Yayin da al'amuran cin hanci suka dabaibaye fannin shari'a a tarayyar da jihohin kasar, hukumar kula da shari'ar ta dauki tsauraren mataki kan was alkalan da ake tuhumu da aikata laifi.

A Najeriya kwararru a fanin shari'a da ma yaki da cin hanci da rahsawa sun mayar da martani a kan sallamar wasu manyan alkalai biyu tare da ladabtar da wasu uku da majalisar hukumar kula da harkokin shari'a na kasar ta yi, saboda cin hanci da wasa da aiki.

Wannan mataki da hukumar kula da harkokin shari'ar Najeriyar ta dauka da ake ganin kama hanyar yi wa sashin shari'ar kasar wankan tsarki ne daga mumunan hali na cin hanci da rashawa da ya samu kansa a ciki, yanayin da ya kai ga manyan jami'an shari'a yarda da cewa adalci a kotu ya zama sai mai kudi a hannunsa.

Hukumar kula da harkokin shari'ar da ta tillasta wa manyan alkalan biyu wato mai shari'a Gladys Olotu, wacce bayanai suka nuna an same ta da kadarori da ma kudade a asusunta da suka kai Naira bilyan biyu. Sannan sai mai shari'a U. A. Inyang wanda shi ma aka sallama bisa zargin cin hanci da rahsawa da ma sakaci da aiki. Yanzu haka dai matakin na zama abin da zai iya samar da sabuwar fata ga talakan Najeriyar, duk da cewa sashin shari'ar ne madafar karshe ta samun adalci a gare shi. Barrista Mainasara Ibrahim, ya ce fatan da suke da ita abin ya dore.

"To motsi yafi labewa, domin an fara samun mataki ne na gyara. Dama ai daya ne daga cikin sassan da suka fi ko wanne sashi gurbata, shi ne sashin shari'a. Alkalai da lauyoyinmu sun mayar da aikin a matsayin wata hanya ce ta kasuwanci, don a samu kudi ba wai ta kamanta adalci ba. Abin takaici ne a ce a Najeriya shari'a ta fi karfin talaka, don ban taba ganin inda talaka ya yi shari'a da mai kudi ba, aka ce talaka ya samu nasara, saboda yadda tsarin yake".

Tazara da batun cin hanci da rashawa ya yi a sashin shari'ar Najeriyar, ya kai ga babu babba ba yaro a harkar. Abin da ya fi daga hankali shi ne yadda kokarin tona asirin masu wannan aiki ke jefa jami'ai cikin tsaka mai wuya, kamar yadda ta faru da tsohon shugaban babbar kotun daukaka karan Najeriyar Ayo Salami, da ya tona asirin karbar cin hanci ga tsohon babban jojin Najeriya Katsina Alu. To sai dai ga Malam Abubakar Ali ya ce duk munin matsalar mafita guda ce kuma tana da sauki.

Ya ce ai "yawa-yawan shugabanin ba su zo da niyyar gyara kasar nan ba, ba su zo da niyyar bauta wa jama'a ba, kai har tsoron Allah basa ji, don da suna ji ai da abin da ke faruwa a yanzu ba zai faru ba. Amma fa gyaran Najeriya a kullum na kan fada cewa ai ba abin da ya fi shi sauki, domin kuwa ba mai kwaikwayon shugabansa irin dan Najeriya. Saboda haka matsalar ita ce a samu shugabanni da za su nuna mulki, su aikata aikin da mutane za su ga misali daga gare su, ba wai su rinka aikata wani abu daban ba".

A yanzu dai hukumar kula da harkokin shari'ar ake ganin ta farga bisa ga nuna hali ba sani ba sabo ga alkalan Najeriyar, abin jira a ganin shi ne tasirin da wannan zai yi wajen zama darasi ga na baya, ta yadda za su gyara zama, ta yadda sashin shari'ar zai zama madafar karshe, ta samun adalci ga talalakan Najeriyar ba wai sai mai kudi ba.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Usman Shehu Usman