Bacin ran kasashe kan harin Birtaniya | Labarai | DW | 23.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bacin ran kasashe kan harin Birtaniya

Yayinda ake ci-gaba da binciken musabbabin harin, hukumomin London sun tsare mutane da yawa, haka kuma kasashen duniya na aika sakonnin jajantawa kasar bayan kai hari a majalisar dokoki a tsakiyar wuraren yawon shakatawa

Shugabannin kasashen duniya na ci gaba da bayyana takaici kan harin majalisar dokokin Birtabiya da wani ya kai a jiya Laraba, tare da yin Allah wadai da lamarin.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta ce Jamus da al'umarta baki daya na tare da Birtaniya a yaki da ayyukan ta'addanci ta ko wane fanni. Haka Shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier ya ce manufar Jamus guda ce da Birtaniyar a yaki da ta'addancin.

Jami'an ‘yan sandan birnin London sun ce suna da bayanai kan mutumin da ya kai harin a jiya Laraba wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 5 tare da jikkatar wasu sama da 40.

Mutumin dai ya kutsa cikin mutane da mota, a kan gadar Westminster inda masu tafiya a kasa suke, kafin daga bisani ya gangara zuwa majalisar dokokin kasar da ke a birnin na London.

Sai dai fa jami'an 'yan sandan ba su bayar da karin bayani kan mutumin da ya kai harin ba.