Babu wata yarjejeniya kan nukiliyar Iran | Labarai | DW | 24.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Babu wata yarjejeniya kan nukiliyar Iran

Rahotanni na nuni da cewar da kyar ne a cimma wata matsaya tsakanin Iran da kasashen da ke da karfin fada a ji a duniya kan batun nukiliyar da ake takaddama akai.

Sassan biyu sun kwashe akalla shekaru 12 suna ta takaddama a kan batun nukiliyar kasar ta Iran. Tuni ma dai kasashen suka fara tunanin kara wa kansu lokaci domin daddale batun na nukiliyar Iran bayan da a wannan Litinin suka shiga rana ta karshe ta wa'adin da aka debar musu domin su cimma yarjejeniya, ba kuma tare da sun samu matsaya a tsakaninsu ba.

Makasudin tattaunawar da suke yi a birnin Vienna dai shi ne samun mafita da za ta kawo karshen takunkumin karya tattalin arzikin da Iran ta kwashe shekaru a cikinsa, wanda kuma ya sanya tattalin arzikin kasar shiga cikin halin tsaka mai wuya. A jawabin da ya yi ga manema labarai, minsitan harkokin kasashen waje na Jamus Frank-Walter Steinmeier ya ce har yanzu akwai gagarumin gibi tsakaninsu da Iran a kan muhimman batutuwa da suka gaza samo mafita.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohamadou Awal Balarabe