Babbar nasara ga Assad a Siriya | Labarai | DW | 20.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Babbar nasara ga Assad a Siriya

Sojojin kasar ta Siriya da kawayensu sun yi galaba a gwabzawar da suke yi da 'yan ta'adda inda suka kwace wani sansanin sojan sama daga hannun mayaka a jihar Idlib.

Wata kungiya da take kiran kanta mai sa'ido kan kasar Siriya, ta ce bisa tallafin jiragen yakin Rasaha, sojan Siriya sun karbe daukacin sansanin mayakan sama da ke birnin Abu Dhuhur, a jihar ta Idlib. Kungiyar ta ce bisa karfin barin wuta ta sama, ya sa 'yan ta'addan Al-Qaida sun gudu suka bar ladansu. Tun sama da shekaru hudu ne dai sojan Siriya suka rasa iko da sansanin mayakan saman.  

Labari mai nasaba.

Mayakan Kurdawan Siriya sun bayyanan cewa jiragen yakin Turkiya sun kai farmaki a wani kauye mai suna Afrin, wanda yankin da suka fi karfi ne a kasar ta Siriya. kakakin mayakan Kurdawa a yankin ya fada wa manema labarai cewa, kawo lokacin rubuta wannan labari babu tabbacin yawan mutanen da suka mutu ko suka jikkata sakamkon harin. Dakarun Turkiya dai sun kai farmakin ne kan tungar mayakan da kasar Amirka ke marawa baya a cikin kasar Siriya. Kasar Rasha ta koka bisa hare-haren da Turkiya ke kai wa dama daukacin shirin Turkiya na kutsawa cikin kasar ta Siriya, inda kasar Rasha ta kai wannan korofin ga MDD.