Babban jinkiri wajen bada sakamakon zaben Nijar | Siyasa | DW | 24.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Babban jinkiri wajen bada sakamakon zaben Nijar

Hankullan al'ummar kasar Nijar da ma na kasashen da ke makwabtaka da ita sun karkata wajen ganin yadda za ta kaya dangane da sakamakon zabukan da suka gudana.

Niger Wahlzentrale Niamey

Inda ake bada sakamakon zaben Nijar

Duk kuwa da cewa tuni 'yan adawar kasar suka yi watsi da shi, hukumar zabe mai zaman kan ta CENI na ci gaba da bayar da sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki da ya gudana na ranar 21 ga watan nan na Febrairu. Sai dai bada sakamakon na tafiyar hawainiya, abun da ke kara sanya aza ayar tambaya kan sahihancin sakamakon da tuni ke shan suka daga bangaran 'yan adawa da suka hadu akarkashin wata gamayyar da suka kira COPA inda suka ce duk wanda ya yi nasara zuwa zagaye na biyu daga cikin su za su taru su kama masa.

A bisa shafin dai na hukumar zaben kasar ta Nijar har ya zuwa ranar wannan Laraba, sakamakon kananan hukumomi 72 ne aka bayar daga cikin 308 da aka yi zaben kasa da kashi 15 kenan cikin 100 na yawan 'yan kasar miliyan 07,5 da ya cancanci su yi zabe sannan kashi 30 na wadanda suka yi zaben. Hakan ya yi karanci sosai kan yadda za a iya gane inda akalar sakamakon ta nufa, ko ficewa tun zagayan na farko kamar yadda Shugaban kasar Issoufou Mahamadou da ke neman wani wa'adi na biyu ya sha nanatawa, ko kuma zuwa zagaye na biyu kamar yadda 'yan adawar suka ce ya zama dole.

A halin yanzu dai bisa sakamakon da ke hannu, Shugaban kasar Issoufou Mahamadou ne ke kan gaba, sannan wasu 'yan takarar uku na biye da shi cikinsu Hama Amadou da ke zaman na biyu da Seini Oumarou da ke sahu na uku, sai Mahamane Ousmane shugaban kasar ta Nijar na farko da aka zaba a shekara ta (1993 zuwa 1996) da ke sahu na Hudu. Ga baki daya dai 'yan takara 15 ne ke neman shugabancin kasar ta Nijar wadda ke da al'ummar da yawan ta ya kai miliyan 18, sannan daya daga cikin kasashe mafi talauci a duniya da ke fama da tarin matsaloli na tsaro a yankin gabashin kasar inda Boko Haram ke tadda kayar baya lokaci zuwa lokaci.

Tuni dai al'umma ta soma nuna kosawarta dangane da jinkirin da ake samu na bayar da sakamakon inda har ya zuwa wannan lokaci ba a sanar da sakamakon jihar Tahoua inda shugaban kasar da ke neman wani sabon wa'adi ke da mafi yawan goyon baya.

Sauti da bidiyo akan labarin