Muhammed Babandede shi ne tsohon shugaban hukumar kula da shige da fice ta Najeriya da ya yi ritaya. A hirar da wakilinmu da ke Abuja Uwaisu Abubakar Idris ya yi da shi sun tattauna a kan batun cin hanci da rashawa a hukumar da rashin tsaro na kan iyakokin Najeriya a daidai lokacin da kasar ke fama da ayyukan 'yan taada da masu kai hare-hare da makamai.