Ba a kama masu hannu a harin Paris ba | Labarai | DW | 19.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ba a kama masu hannu a harin Paris ba

Rahotanni daga kasar Faransa na nuni da cewa har kawo yanzu ba a kai ga gano inda wadanda ake zargi da kitsa harin da aka kai a birnin Paris na kasar ba.

Abdelhamid Abaaoud wanda ake zargi da kitsa harin Paris

Abdelhamid Abaaoud wanda ake zargi da kitsa harin Paris

Bayannan da ke fitowa daga kasar sun tabbatar da cewa daga cikin mutane bakwai da jami'an tsaron Faransan suka yi nasarar cafkewa a wannan Larabar, babu Abdelhamid Abaaoud da kuma Salah Abdeslam, wadanda aka hakikance suna da hannu a harin na birnin Paris da ya hallaka mutane 129. A kallah mutane biyu ne suka mutu a yayin samamen da jami'an tsaron suka kai wani gida a yankin Saint Denis da ke kusa da birnin na Paris, ciki kuwa har da wata mace da ta tayar da abubuwa masu fashewa a jikinta yayin da dayan kuma ya mutu sakamakon harbin bindiga. Jami'an tsaron dai sun cafke mutane bakwai a yankin na Saint Denis a yayin wannan samame.