Azumi da addu′oi a Saliyo sakamakon Ebola | Labarai | DW | 01.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Azumi da addu'oi a Saliyo sakamakon Ebola

A jawabinsa na sabuwar shekara ta kafar yada labarai, shugabaBai Koroma na Saliyo ya bukaci a shiga azumi da adduo'i na mako guda tun daga ranar Alhamis din nan.

Shugaba Ernest Bai Koroma na Saliyo ya bukaci al'ummar kasar su gudanar da azimi na tsawon mako guda tare da yin addu'oi don neman tallafin mahalicci a yakin da ake yi da annobar Ebola.

Wannan bala'i dai na Ebola dake ci gaba da lakume rayukan al'umma a yammacin Afrika a wannan karo na zama mafi muni a tarihin cutar, musamman a kasar ta Saliyo a yanzu. Yawan mutanen da suka rasu a duniya ta sanadin cutar ya haura 20,000 kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana.

Saliyo ita ce kasar da wannan cuta ta Ebola tafi muni inda aka sami mutane sama da 9,000 da suka harbu da kwayoyin wannan cuta kuma take ci gaba da kama mutane.