Azabtar da fursinonin Iraki a hannun sojan Birtaniya | Siyasa | DW | 20.01.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Azabtar da fursinonin Iraki a hannun sojan Birtaniya

Wasu hutuna da aka gabatar baya-bayan nan a nan Jamus sun nuna yadda sojojin Birtaniya ke azabtarwa da kuma cin mutuncin fursinoni farar fula a kasar Iraki

Sojan Birtaniya na azbtar da wani fursunan Iraki farar fula

Sojan Birtaniya na azbtar da wani fursunan Iraki farar fula

An saurara daga wani dake aika wa da tashar BBC rahotanni daga birnin Bagadaza yana mai fadin cewar wadannan hotuna dai sune suka rika mamaye kannun labarai a kasashen Larabawa tun bayan da aka fallasa wannan tabargaza ta azabtarwa da cin mutuncin fursinoni farar fula na kasar Iraki a hannun sojojin Birtaniya. A cikin sharhunan da suka rika bayarwa, masharhanta na kafofin yada labaran kasashen Larabawa sun janyo hankalin mutane zuwa ga gaskiyar cewa wadannan fa ba sojojin Amurka ne a kurkukun Abu Ghuraib ba, sojan Birtaniya ne ke da alhakin wannan cin mtunci da muzantawa na ba gaira ba dalili. Wannan mummunar tabargaza ce dake shafa wa manufofin diplomasiyyar Birtaniya kashin kaza, in ji Emily Buchanan, mai aike wa BBC rahotanni akan manufofin tsaron kai. Su dai sojojin Birtaniya da farko an yaba musu salla ne, amma sai suka kasa alwala. Domin kuwa da farkon fari an sha yayata cewar sojojin suna da da’a da halin sanin ya kamata da kuma wata dadaddiyar hulda da sauran jinsunan mutane a kasashen ketare. Amma wannan tabargazar ta azabtar da fursinoni farar fula ta sanya murna ta koma ciki a game da koda sojan Birtaniyar da ake yi. Jim kadan bayan da P/M Birtaniya Tony Blair ya fito fili yana mai la'antar matakan azabtar da fursinoni da sojan Amurka suka dauka a kurkukun Abu Ghuraib shekarar da ta wuce, wasu hotunan sun billo dangane da sojan Birtaniya. Kuma ko da yake a wancan lokaci an ce wai wadannan hotuna na jabu ne, amma suka shafa wa sojan Birtaniyar kashin kaza. An saurara daga tsofon janar na sojan Birtaniya Sir Mike Jackson yana mai nuni da cewar wadannan sojojin ba su cancanci saka rigar sarki ba. Amma abin da zai kara munana lamarin shi ne idan har a zaman shari’ar aka gano cewar sojojin sun bi umarni ne da aka ba su, ba kawai sun dauki matakin ne bisa radin kansu ba. Bayan la’antar dukkan nau’in matakin azabtarwa da cin mutuncin fursinoni Sir Mike Jackson ya ce za a bididdigin lamarin daga tushensa, saboda Birtaniya ba zata yarda wasu ‚yan tsiraru su shafa wa sojan kasar su kimanin dubu 65 da aka tura zuwa Iraki tun bayan billar yakin kasar ba. Jami’an siyasar Birtaniya dai na fargaba a game da tasirin da wadannan hotuna zasu yi a dangantakar kasar da sauran kasashe na Larabawa. Domin kuwa rahotanni sun ce akwai wasu hutunan ma da aka ki fitowa da su saboda ba su da kyan gani ko kadan. A can kasar Irak dai al’amuran tsaro sai dada tabarbarewa suke yi a daidai lokacin da ake shirye-shiryen gudanar da zabe, inda a jiya laraba aka halaka wasu mutane 26 a wasu hare-hare na kunar bakin waken da aka kai. Bugu da kari kuma, bayan nuna wadannan hutuna da aka yi, a yanzu sojojin Birtaniya zasu rika fuskantar barazana wajen gudanar da ayyukansu a Basra da kewayenta.