Ayyukan agaji bayan girgizar kasa a China
April 21, 2013Talla
Dubban masu aiyukan ceto sun yi dirar mikiya a garuruwan da ke yankin kudu maso yammacin kasar China, inda girgizar kasa mai karfi maki 6.6 a wannan Asabar da ta gabata, ta hallaka kusan mutane 200.
Dubban sojojin da aka tura sun kwashe dare su na aikin neman masu sauran nunfashi, kuma firaministan kasar Li Keqiang ya kai ziyara a wajen da abun ya faru, domin ganin yadda aiyukan agajin ke gudana. Akwai wasu mutane fiye da 6,700 da suka samu raunuka sanadiyar girgizar kasar ta China.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Zainab Mohammed Abubakar