1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru ta karbi rance daga asusun ba da lamuni domin Corona

Binta Aliyu Zurmi
May 5, 2020

Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya amince da bai wa Jamhuriyar Kamaru rancen kudi na dala miliyan dari biyu da ashirin da shida domin yaki da annobar Coronavirus.

https://p.dw.com/p/3bmH0
USA Weltbank-Zentrale in Washington
Hoto: Reuters/Y. Gripas

A wani mataki na tallafa wa kasashe da ke da raunin tattalin arziki daga durkushewa sakamakon annobar Corona, asusun ya rubanya tallafin da ma ba da umurnin bai wa kasashen kudin cikin gaggawa. Kasancewar kasar ta Kamaru ita ma tana fuskantar matsin tattalin arziki. Gwamnatin  ta Kamaru na kokarin yaki da wannan annoba ta hanyar inganta harkar lafiya da ma  farfado da tattalin arzikin kasar.