Asarar rai a bikin sabuwar shekara a China | Labarai | DW | 01.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Asarar rai a bikin sabuwar shekara a China

Mutane 35 sun hallaka bayan da aka samu wani turmutsutsu da aka yi wajen yin shagalin shigowar sabuwar shekara a birnin Shanghai na kasar China.

Da misalin karfe sha biyu na daren jiya dai an gudanar da irin wasan wuta din nan na fire works da bukukuwa a sassa daban-daban na duniya don marabtar sabuwar shekarar ta 2015.

To sai dai lamarin ya zo da sammatsi a kasar China inda mutane 35 suka rasu sakamakon wani turmutsustu da aka yi wajen bukukuwan sabuwar shekarar a dandalin nan na Chen Yi da ke Shanghai.

Kamfanin dillancin labaran China na Xinhua ya ce yanzu haka mahukuntan kasar na gudnar da bincike don tantance hakikanin gaskiyar dalilin wannan hadari da aka gamu da shi.