Armenia da Azerbaijan za su yi sulhu | Labarai | DW | 10.10.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Armenia da Azerbaijan za su yi sulhu

Bayan kusan makonni biyu na dauki ba dadi tsakanin Armeniya da Azerbaijan, kasashen sun cimma kwarya kwaryar yarjejeniya tsakaita bude wuta domin tattauna rikicin yankin Nagorno-Karabakh.

Kungiyar agaji ta Red Cross mai shiga tsakanin kasashen biyu a birnin Moscow, ta ce bangarorin biyu sun amince da musanyar fursunoni a wani mataki na kawo karshen rikicin.

An samu asarar rayukan fararen hula da dama, yayin da wasu suka yi hijira saboda fargabar barkewar yaki bayan da kasashen Rasha da Turkiyya suka shiga rikicin.