Arewa ta sake yin gwajin makamin nukiliya | Labarai | DW | 29.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Arewa ta sake yin gwajin makamin nukiliya

Rahotanni daga Koriya ta Arewa ta harba wani makami mai linzami wanda a wani gwaji da ta wanda ya bi ta cikin kasar Japan kana ya fada cikin Tekun Pacific a wannan Talatar.

Sabon da gwajin makamin da mahukuntan na Pyongyang suka yi dai ya harzuka gwamnatin Japan wadda ta ke cewar wannan gwajin makamin wata barazana ce ga Tokyo. Masu aiko da rahotanni suka ce tuni Japan din ta bukaci Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya yi zama na musamman kan wannan batu da nufin daukar mataki kan Koriya ta Arewan kafin lamura su rincabe. Wannan dai shi ne karon farko da Arewan ta yi gwajin makami mai linzami da ya kusanci wata kasa da ke dasawa da Amirka.