Antony Blinken na ziyara a Gabas ta Tsakiya | Labarai | DW | 25.05.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Antony Blinken na ziyara a Gabas ta Tsakiya

Sakataran harkokin wajen na Amirka Antony Blinken ya isa a birinin Tel Aviv na israila a wani mataki na rangadi a yankin gabas ta Tsakiya da nufin samar da shirin tsagaita wuta tsakanin Isra'ilan da Falasdinu.

US Antony Blinken in Israel mit Gabi Ashkenazi in Tel Aviv

Antony Blinken tare da ministan harkokin waje na Isra'ila Gabi Ashkenazi

Atony Blinken wanda zai gana da da firaminstan Isra'ila Benjamin Netanyahu da kuma jagoran Falasdinawa Mahmud Abbas. zai  yi kokarin jadadda musu muhimmanci dakatar da fadan da sasan biyu ke gwabza kusan kwanaki goma wanda a ciki aka samu asarar rayuka mai dimbi yawa. Sai dai kawo yanzu duk da irin yunkurin diplomasiyar da ake ci gaba da yi ana ci gaba da yin tashin hankalin tsakanin bangarorin biyu musammun ma a yankin zirin gaza da ke a karkashin ikon Hamas