1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Nijar: Barkewar annobar amai da gudawa

August 10, 2021

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta bayyana barkewar annobar cutar amai da gudawa ko Cholera a wasu jihohi uku na kasar.

https://p.dw.com/p/3ynPx
Niger - Gesundheitsstation in Garin Goulbi
Mutane da dama ne dai cutar amai da gudawar ta shafa a jihohin uku na NijarHoto: picture-alliance/dpa/T. Schulze

Kawo yanzu kimanin mutane 12 ne annobar ta yi sanadiyar mutuwarsu. Yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a Yamai fadar gwamnatin kasar, ministan kiyon lafiya na Jamhuriyar ta Nijar Dakta Iliyassou Idi Mainassara ya yi karin haske kan barkewar annobar cutar amai da gudawar. Ministan ya nunar da cewa a yanzu haka cutar ta yi kamari a jihohin Maradi da Damagaram da Dosso.

A jihar Damagaram, annobar ta barke a cikin yankin Tanout da Magarya da Damaram ta Kaya da Mirya. A jihar Maradi kuwa annobar ta barke a cikin gundumar Madarunfa da Gidan Rumji da Maradi Gari, sai jihar Dosso inda aka samu barkewar annobar a  gundumar Gaya da Dogon Dutsi. Kawo yanzu a cewar Minista mutane 213 ne suka kamu kuma 12 cikinsu cutar ta yi ajalinsu.