Annan ya yi kira da a aika da tawagar kwararru zuwa Darfur
December 12, 2006Talla
Hukumar kula da kare hakin Bil Adama ta MDD ta kammala zagaye na farko na taro na musamman da take yi a birnin Geneva, akan halin da ake ciki a lardin Darfur na yammacin Sudan. A gobe laraba za´a ci-gaba da taron wanda KTT ke daukar nauyin gudanarwa. A wani sako na bidiyo da ya aikewa zaman taron na yau, babban sakataren MDD mai barin gado Kofi Annan ya yi kira da a tura wata tawagar kwararru mai zaman kanta zuwa yankin. Mista Annan ya ce ya zama wajibi a dauki dukkan sahihan matakai don kawo karshen kisan kare dangi da ake yi a wannan lardi.