Angela Merkel zata gana da Vladimir Putin | Labarai | DW | 02.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Angela Merkel zata gana da Vladimir Putin

Shugabannin Jamus da na Rasha za su gana don duba yiwuwar daidaita rikicin Syria da Ukraine a daidai lokacin da ake shirye-shiryen taron manyan kasashe G20 nan gaba kadan a Jamus.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha za su tattauna batun taron kasashen G20 masu karfin masana'antu da za a yi cikin watan Yuli a birnin Hamburg na nan Jamus. A ziyarar ta biyu da Merkel ke kaiwa Crimea tun shekara ta 2014, za kuma ta dubi rikicin gabashin Ukraine da kuma na Siriya, kamar yadda kakakin Angela Merkel ya tabbatar.

Shugabar gwamnatin Jamus dai ta shirya ganawa da jagororin manyan kasashen na G20 gabanin taron na watan Yuli. Ganawar ta wannan Talata a Rasha, na zuwa ne mako 'yan kwanaki bayan mutuwar wani jami'in kungiyar nan ta tsaro da hadin kan Turai a gabashin Ukraine, yankin da 'yan tawaye masu goyon bayan gwamnatin Rasha ke gwagwarmaya da makamai.