Angela Merkel na fuskantar kalubale | Siyasa | DW | 28.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Angela Merkel na fuskantar kalubale

Matakan da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ke dauka dangane da 'yan gudun hijira na cigaba da harzuka jama'a har ma da 'yan jam'iyyarta ta CDU wadanda kansu ke rabe dangane da batun.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel

Wannan matsala dai ta sa mutane shakkun ko za ta iya jure kalubalen da ke gabanta na samun hadin kai a manufofin 'yan gudun hijirar. Shugabar gwamnatin Jamus din na ci gaba da shan suka ba kakkautawa, ko da yake ta bukaci da a karfafa 'yancin samun mafaka ga duk wadanda ke neman mafaka, ta kuma jaddada mahimmancin da ya ke da shi a tasa keyar duk wanda bai sami 'yancin zaunawa a kasar ba. Baya ga haka ta ce za ta kara yawan kudin ga jihohi da kananan hukumomin da ke fuskantar rikicin 'yan gudun hijirar.

Kakkausar suka daga jam'iyyar CDU

Sai dai akwai shakkun ko wadannan kudade za su isa, inda har a jam'iyyarta ma ta Christian Democratic Union ake sukarta fiye da yadda aka taba yi har ma masana siyasa irinsu Oskar Niedermayer na ganin cewa batun gudun hijirar zai kasance wani gwaji na kwarjininta a jam'iyya.

Yanayin kan iyakar Jamus da Ostiriya

Yanayin kan iyakar Jamus da Ostiriya

"Akwai alamu mabanbanta daga jam'iyyar a waje guda, daga al'umma da jihohi har ma da wani bangaren 'yan majalisa, ana ci gaba da sukan manufofin 'yan gudun hijirar na Merkel, a yayin da a daya bangaren kuma muna jin cewa tana samun goyon baya daga kalilan na al'umma da ma wasu jami'an gwamnati. Wannan na nufin cewa jam'iyyar ta rabu gida biyu kamar dai yadda su ma 'yan kasar suka rabu."

'Yan maganganu masu ba da karfin gwiwar da take yi tana cewa zamu iya yi! yana ci ma wasu tuwo a kwarya, sannan bayan da ta dauki hoto da wani dan gudun hijira irin wanda ake cewa Selfie a turance, da yawa a jam'iyyar suka fara mata kallon wadda ba ta san ainihin me ake ciki ba. Sai dai akwai wadanda ke ganin cewa lallai hanyar da ta dauka dai-dai ne. Mai kula da shirin kawo karshen matsalar 'yan gudn hijira Peter Altmaier ya ce akwi kyakyawar fata:

Kakkyawan fata da kwarin gwiwa

"Duk wadanda na tattauna da su, sun shaida min cewa mutane da dama a ciki da wajen jam'iyya sun yarda da manufofin shugabar gwamnatin, dan babu wanda ya yi amannar cewa akwai wanda zai iya kula da wannan matsalar fiye da ita Angela Merkel din. Shi ya sa muka yi amannar cewa za mu shawo kan wannan kalubalen, ba wai a matsayin batun 'yan gudun hijirar kawai ba, har ma da karbuwar da ake bukata daga wajen 'yan kasa"

Dubban 'yan gudun hijira na ci gaba da shiga Jamus

Dubban 'yan gudun hijira na ci gaba da shiga Jamus

Ita ma ministar tsaro Ursula Von der Leyen ta bayyana makamancin haka a kafofin yada labarai, sai dai batun na ci gaba da daukar zafi a cikin jam'iyyarta inda ake kyautata zaton cewa yanayin zabe ka iya sauyawa. Axel Eduard Fischer Dan majalisane daga jam'iyyar CDU ya kuma ce:

"Daga karshe dai, ya kamata mu iya fada a baiyane cewa, Jamus ba za ta iya kawo karshen matsalar talauci a duk duniya ba, kuma ana sa ran ganin shugabar gwamnatin ta yi abu dangane da hakan fiye da abin da ta yi a yanzu."

Masana siyasa irinsu Oskar Niedermayer, na da ra'ayin cewa ba wai Merkel ba ta yin iya kokarinta wajen bayyana sauya alkiblar da suka yi a fannin 'yan gudun hijira ga al'umma ba ne, sai dai abin na kama da cewa sakon baya zuwa.

Sauti da bidiyo akan labarin