Ana zargin gwamnatin Chadi da take hakki | Siyasa | DW | 13.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ana zargin gwamnatin Chadi da take hakki

Kungiyar Amnesty International ta nuna damuwa kan yadda ake ci gaba da samun take hakkin bil-Adama a kasar Chadi tun bayan zaben shugaban kasar.

Bayan zaben shugaban kasar da aka yi mai cike da rudani da ya bai wa Idriss Deby Itno damar sake darewa kan karagar mulkin kasar. Kungiyar da ke kare hakkin dan Adam ta ce ana cin zarafin 'yan adawa, da 'yan fafutika da kuma wakillan kungiyoyin fararen hulla. Kuma kungiyar nan ta IYINA tana kan gaba wajen fuskantar kamun mambobinta. Sannan ga cin zarafin da aka yi wa Mahmat Alhabo wani dan adawa na kasar ta Chadi.

Jagoran kungiyar FONAC, hadin gwiwar kungiyoyin adawa a kasar ta Chadi, ya dawo ne daga bulaguron da ya kai a kasashen waje, kuma ya yin saukarsa a filin jirgin sama, Mahmat Alhabo ya ce ya ga tashin hankali tare da cin mutunci daga jami'an tsaro na asiri na kasar ta Chadi.

Bayan 'yan mintoci ne jami'an tsaron suka mika masa kayansa, sai dai ba duka ba. Dan adawan na kasar Chadi ya yi Allah wadai da tozartawa da ya ce jami'an tsaron kasar sun yi masa, kuma yana da shirin shigar da kara a gaban kotu dangane da halayen da jami'an tsaron asirin suka nuna a kan shi. Inda ya ce a cikin kasa da take kiran kanta ta Demokaradiyya, amma kuma jami'an tsaro na 'yan sanda na yin abun da suka ga dama ba tare da sun fuskanci hukunci ba. Matakin da a cewarsa na daga cikin cikin irin halin mulkin kama karyan da gwamnatin ta yanzu ke yi a kasar ta Chadi.

A watan Febrairu ma dai da ya gabata, daliban jami'a 69 ne aka tsare a gidan kaso na tsawon wata guda bisa zargin batanci ga hukumar kasa bayan da suka kawo tsaiko ga wata ziyara ta ministoci yayin wata zanga-zanga da suka yi kan soke kudadan alawus din da ake basu. Kungiyar Amnesty International ta nuna damuwarta sosai kan halin da ake ciki na matsi a kasar ta Chadi, inda ta ce an samu kame-kame masu yawan gaske daga bangaran 'yan fafutika masu adawa da manufofin gwamnati na kungiyar IYINA. Sai dai tuni ministan tsaron cikin gidan kasar ta Chadi ya yi watsi da wannan zargi na take hakin jama'a inda ya ce kamun abu ne da suka yi shi bisa gaskiya.

A labaran baya-bayan nan dai an ce a saki matasan 'yan gorgormayawar guda 12 sai dai kuma har yanzu jagoransu Nadjo Kaina, na ci gaba da kasancewa a tsare a wani wurin da ba a san ko ina ne ba a cewar kungiyar kasa da kasa ta Amnesty Internationl mai fafutikar kare hakin dan Adam.

A hannu daya kuma a daren Talata wayewar Laraba, wasu mutane da ba a san ko suwanene ba sun yi kwanton bawna inda suka kashe wasu sojojin kasar ta Chadi guda akalla guda 10 bayan da aka kamasukuma ake bisa hanyar kaisu gidan kaso da ke arewacin kasar a cewar wata majiya ta jami'an tsaro kasar. Inda ta ce wasu mutane ne dauke da bindigogi cikin wasu manyan motoci marassa lambobi, suka tare motar 'yan kason suka kuma fito da sojoji kafin daga bisani su yi musu ruwan harsashai.

Sauti da bidiyo akan labarin