1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana zabe karo na uku a Isra'ila

March 2, 2020

An bude rumfunan zabe a Isra'ila a wannan Litinin, a wani zaben da Firaminista Benjamin Netanyahu ke cewa yana kokari ne na kawo karshen rikita-rikitar siyasar kasar.

https://p.dw.com/p/3YiKf
Symbolbild: Präsidentschaftswahlen in Israel 2019
Hoto: Getty Images/AFP/M. Kahana

Wannan ne dai  karo na uku da ake zabe cikin kasa da watanni 12 a Isra'ilar, kuma makonni biyu gabanin shari'ar da ke gaban Mr. Netanyahu da ke fuskantar zarge-zarge na cin hanci da rashawa.

Ana sa ran a zaben da mutane miliyan shida da dubu 400 za su kada kuri'a, takara za ta yi zafi tsakanin jam'iyyar Likud da ta Blue and White, inda kowane bangare ke nuna alamun da wuya ne ya yi galaba da wani rinjaye a majalisar kasa.

Ko a zaben kasar da aka yi a watannin Afrilu da Satumbar bara ma dai, babu wata jam'iyyar da sami rinjaye kai tsaye.