Ana shari′ar sojoji kusan 600 a Najeriya | Labarai | DW | 20.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana shari'ar sojoji kusan 600 a Najeriya

Shari'ar na zuwa ne daidai lokacin da wasu sojojin ke fuskantar shari'a bisa zarginsu da laifuffuka daban-daban a yakin da ake yi da Kungiyar Boko Haram.

Rundunar tsaron Najeriya ta sanar da gabatar da jami'anta wajen 600 a gaban kotun soji na musamman, a daidai lokacin da wasu sojojin ke ci gaba da fuskantar shari'a bisa zarginsu da laifuffuka daban daban a yakin da ake yi da Kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Mai magana da yawun rundunar sojin Kanar Sani Usman ya ce kimanin jami'ai 579 ne aka gurfanar da su yau a gaban kotun sojin a birnin Abuja, domin gaggauta zartar da hukunci mai adalci, sai dai ya ki karin haske wa 'yan jarida dangane da shri'ar da ma lokacin da aka fara shi.

A shekarar da ta gabata kotun sojin ta yanke hukuncin kisa akan sojoji guda 72, saboda abun da ta kira samunsu da laifufuka da suka hadar dana cin amanar kasa, taimakawa abokan gaba da wasu da ke da nasaba da yaki da Boko Haram.

Lauyan kare hakkin jama'a Femi Falana ya yi Allah wadan wannan hukuncin da ma ita kanta shari'ar da ake yi a asirce, saboda acewarsa hujjojin wadanda yake karewan sun bayyana irin yadda cin hanci da karbar rashawa ya mamaye rundunar tsaron Najeriyar, inda manyan jami'ai ke karkata kudaden albashi dana kayan aiki zuwa aljihunsu.