Ana samun galaba kan mayakan IS a Iraki | Labarai | DW | 23.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana samun galaba kan mayakan IS a Iraki

Rundunar sojin Iraki ta ce ta karbe iko da wani yanki da ke gabashin Ramadi wanda 'yan kungiyar nan ta IS suka karbe iko da shi a yunkurinsu na girka daular Islama.

Irak Milizen

Sojin Iraki sun samu wannan nasara ce da taimakon soji sa kai na Sunni da na 'yan Shi'a

Wani jami'in tsaro da ya zanta da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP bisa sharadin za a sakaye sunansa ya ce yanzu haka dakarun gwamnati ne ke iko da yankin Husaybah kuma sun danna kai don kubutar da lardin Jweibah.

Wannan nasara da sojin Iraki suka samu tare da tallafin sojin sa kai da ke bin tafarkin Sunni da Shi'a a yankin na zuwa ne daidai lokacin da dakarun kawancen da Amirka ke jagoranta a yaki da 'yan IS ke kara matsa kaimi wajen kai hari kan mayakan IS din a Ramadi tun daga jiya Juma'a.