Ana kokarin cimma tudun dafawa a taron kungiyar WTO a Hongkong | Labarai | DW | 18.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana kokarin cimma tudun dafawa a taron kungiyar WTO a Hongkong

Da akwai alamar cewa za´a cimma wata yarjejeniya to sai dai ba ta karshe ba a taron kolin kungiyar cinikaiya ta duniya WTO da za´a kammala yau lahadi. Ministan ciniki na Indiya Kamal Nath ya nunar a gun taron da ke gudana a Hongkong cewa an kusa cimma yarjejeniya kuma wakilin Amirka a harkokin cinikaiya Rob Portman ya nuna kyakyawan fatan cimma tudun dafawa bisa manufa. To sai dai wata sabuwar adawa da Brazil ke nunawa na barazanar kawo cikas ga kokarin samun wata masalaha akan manufar sakarwa harkokin kasuwanci mara. A jiya asabar kwamishinan cinikaiya na tarayyar Turai Peter Mandelson ya ce ana iya soke tallafin da ake ba manoma a shekara ta 2013 duk da cewa Amirka da Brazil sun ba da shawarar daukar wannan mataki a shekara ta 2010. Taron na Hongkong dai ya ci karo da zanga-zanga da tashe tashen hankula mafi muni cikin shekaru gwammai na tarukan kungiyar WTO. Daukaci ´yan kasar KTK masu adawa da hadakar maufofin kasuwancin duniya sun yi ta arangama da ´yan sanda. Akalla mutane 100 sun samu raunuka yayin da aka kame 900 lokacin da ´yan sanda suka hana masu zanga-zangar kutsawa kusa da zauren taron.