1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Ana kada kuri'a a zaben kasar Isra'ila

March 23, 2021

A wannan Talatar, Isralawa na zaben 'yan majalisar dokokin da zai tabbatar da sabon Firaminista bayan rugujewar zabukan da aka yi sau uku a baya.

https://p.dw.com/p/3qzDl
| Israel Hohe Beteiligung bei Parlamentswahl trotz Coronavirus | Benjamin Netanyahu und seine Frau
Hoto: Imago-Images/Xinhua/Shang Hao

An bude rumfunan zabe a Isra'ila, inda 'yan kasar za su yi zaben 'yan majalisar dokoki karo na hudu cikin tsukin shekaru biyu.

Mutane da dama dai na fargabar cewa da wuya ne jam'iyyar Firaminista Benjamin Netanyahu ta kafa gwamnati.

Ana dai kallon zaben na wannan karon ma dai ya kai ga sai an kafa gwamnatin hadaka a Isra'ilar. 

Kuri'ar jin ra'yi dai ta nuna yiwuwar jami'iyyar Mr. Netanyahu ta Likud ta samu 'yar galaba a majalisar, sai dai da wuya ne Fimanistan ya iya kafa gwamnati mai karfi.

Gwamnatin Isra'ila ta karshe ta wargaje ne a watan Disambar bara sakamakon rashin jituwa tsakanin Mr. Netanyahu da madugun adawa Benny Gantz da suka yi hadin gwiwa wajen kafa ta.

A wannan zaben ne kuwa Falasdinawa ke samun damar kada kuri'a, a karon farko cikin gomman shekaru.